Kaza da shanshani - African Storybook Project

Transkript

Kaza da shanshani - African Storybook Project
Kaza da
shanshani
Plan Niger - Projet
NECS - Usaid, Avec
la contribution du
and Avec la
contribution du
Comité ASL
Winny Asara
Hausa
Kaza da shanshani abokai ne. Amma
kullum suna takara tsakaninsu. Wata
rana, sai suka yi niyyar wasan ƙwallon
ƙafa don sanin wa ya fi kwaninta
tsakani su biyu(2).
1
Sai suka shiga filin ƙwallon ƙafar kuma
suka fara wasan. Kaza tana da
gaugawa amma shanshani ta fi ta
gaugawar. Kaza ta harba ƙwallon
nesa amma kuma shanshani tana
aika ƙwallon neza ƙwarai fiye inda na
kazar zai je. Ganin haka, sai kaza ta
fara hassala.
2
Ƴan takarar biyu (2) sun yi niyyar su je
bugun da kai sai mai tsoron gida. Da
farko shanshani ita ce mai tsaron gida
wato gola kenan. Kaza ta saka ƙwallo
ɗaya rak cikin raga. Sai aka juya, kaza
ta zama gola mai tsaron gida.
3
Shanshani ta harba ƙwallo, kuma ta
saka a raga. Shanshani tana gwaninta
kuma tana saka ƙwallon. Shanshani ta
saka ƙwallon har da kai. Shanshani ta
saka ƙwallon biyar (5).
4
Kaza ta hassala da rishin nasarar da
ta yi. Kaza ba ta iya wasa ba.
Shanshani ta yi ta dariya saboba
abokiyarta ta hassala wajen wasa.
5
Sai kaza ta buɗe babban bakinta ta
haɗiye shanshanin.
6
Lokacin da kaza tana shigowa gida,
sai ta gamu da uwar shanshani. Sai ta
ce mata, “ba ki ga ɗiyata ba?”
Kaza ba ta amsa mata ba. Uwar
shanshani ta damu.
7
Sai uwar shanshani take ji wata
ƙaramar murya tana cewa: “Ki agaje ni
uwata!” Shanshani take faɗi.
Uwar shanshani ta duba kewayenta
da kyau. Muryar nan da cikin kaza ta
fito.
8
Uwar shanshanin ta yi ihu “Ki yi
amfani da duk azirinki ɗiyata!”
Shanshani ta saki wani wari. Sai kaza
ta fara jin wani ciwon ciki.
9
Kaza ta yi gyatsa. Kuma ta yi kaki. Ta
yi attishewa kuma take ta tari, take
tari. Shanshani bai ciyuwa!
10
Kaza ta yi ta tari sai ta kako
shanshanin da yake cikin cikinta.
Shanshanin da uwarta sun tafi sun
ɓoye cikin wani icce.
11
Tun daga shi, kaza da shanshani ba su
shiri.
12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Kaza da shanshani
Author - Winny Asara
Adaptation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid, Avec la contribution du and Avec la contribution
du Comité ASL
Illustr
Illustration
ation - Winny Asara
Language - Hausa
Le
Level
vel - Longer paragraphs
© African Storybook Initiative, 2014
Creative Commons: Attribution 4.0
Sour
Source
ce www.africanstorybook.org

Benzer belgeler

Tayaka murnar sayan Sony Ericsson W760i. Siririyar waya mai salo

Tayaka murnar sayan Sony Ericsson W760i. Siririyar waya mai salo Karanta Jagororin don aminci da ingantaccen amfani da babukan garanti mai iyaka kafin amfani da wayarka. Wayarka ta hannu tana da damar saukewa, ajiyewa da tura žarin abun ciki, misali, sautunan ri...

Detaylı